Jamus da Faransa sun buƙaci tura jami´an tsaron ƙasa da ƙasa a Kirgistan
July 17, 2010Jamus da Faransa sun yi kira ga ƙungiyar tabbatar da tsaron ƙasashen Turai da ta tura 'yan sandan tabbatar da zaman lafiya a ƙasar Kirgistan.
A wani taron ministocin ƙasashen Turai da ke gudana a kazakhstan, ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle da takwaransa na Faransa Bernad Koucher, sun bayyana fatan samar da 'yan sandan zai taimaka gaya, wajen inganta halin tsaro a ƙasar da tayi fama da tashin hankalin siyasa da ƙabilanci a kwannan nan tsakanin ƙabilar Uzbek da Kyrgiz wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane a ƙalla 2000.
A jiya Juma'a ne dai ƙungiyar samar da tsaron a Turai da gwamnatin wucin gadin Kirgistan suka amince da tura jami'an tsaro 52 har na tsawon wata huɗu kana daga bisani a ƙara yawan su da wasu 50, domin bada shawara akan hanyoyin tabbatar da tsaro a ƙasar.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Yahouza Sadissou Madobi