Jamus da China na kokarin habaka hudar Diplomasiya | Labarai | DW | 08.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da China na kokarin habaka hudar Diplomasiya

Ministan harkokin wajen Jamus da yanzu haka ya ke wata ziyarar aiki a kasar China domin kara karfafa dangantakar diplomasiya ya ce a kwai bukatar China ta taimaka ta fuskar tsaro.

Kazalika Frank-Walter Steinmeier ya ce China na da matukar mahimmanci wajen bada tallafin da ake bukata a bangarorin sasanta rikicin Siriya.

A yayin taron manema labarai a Beijing a yau juma'ar nan ya kara da cewar:

''China yanzu haka a karon farko ta aike da jakadan ta na musamman zuwa Siriya wanda ya nuna karara irin muradin da suke dashi wajen warware rikicin kasa da kasa,China na kuma bukatar bada tallafin warware rikicin da muke matikar bukatar sa.''

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen China Wang Yi ya ce China zata cigaba ya yaki da cin hanci da rashawa gami da kara hubbasa wajen taka rawar warware rikicin kasar Siriya.