1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu neman mafaka daga Gabashin Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 17, 2016

Majalisar zartaswar Jamus ta dage zaman tattaunawa kan batun al'ummar kasashen yankin Gabashin Afirka, da ke zuwa Turai musamman ma Jamus domin neman mafaka.

https://p.dw.com/p/1J8rO
Zauran majalisar zartaswar Jamus a Berlin
Zauran majalisar zartaswar Jamus a BerlinHoto: Imago/IPON

Majalisar zartaswar ta Jamus dai ta shirya tattaunawa a wannan Litinin din domin ayyana kasashen Moroko da Aljeriya da kuma Tunisiya a matsayin kasashen da suke zaune lafiya, wadanda kuma basa bukatar a basu mafaka. Ko da yake akwai wadanda ke ganin cewa har kawo yanzu al'ummar kasashen ka iya zuwa domin neman mafaka duba da yadda ake ci gaba da samun rahoton take hakkin dan Adam. Idan dai har majalisar zartaswar ta Jamus ta amince da wannan kudiri, to 'yan wadannan kasashe uku da ke zuwa neman mafaka a Jamsu ka iya rasa wannan damar.