1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ci gaba da bincike kan harin Münster

Gazali Abdou Tasawa
April 8, 2018

Hukumomin shari'a a Jamus sun ce har yanzu masu aikin bincike ba su gano dalillan da suka sa Bajamushen nan ya kai hari da mota kan taron jama'a a birnin Münster inda ya halaka mutane biyu ya kuma jikkata wasu 20. 

https://p.dw.com/p/2vgDn
Deutschland Münster Attacke mit Campingbus | Polizei vor Wohnung des Täters
Hoto: Getty Images/AFP/M. Gottschalk

A cikin wata sanarwa da mai shigar da kara na birnin na Münster ya fitar a wannan Lahadi ya ce duk da yake ya zuwa yanzu babu wasu alamun da ke nuni da cewa harin ta'addanci ne irin na masu kaifin kishin Islama, suna ci gaba da binciken duk hanyoyi musamman na batun tabin hankali da mutuman ke da domin fahimtar dalilin mutumin na aikata wanann aika-aika. 

Tun da sanyin safiyar wannan Lahadin mazauna birnin na Münster sun yi ta kai ziyara wurin da lamari ya wakana, tare da ajiye furanni na nuna alhinin ga mutanen da suka mutu a cikin harin.

A jiya Asabar ne dai mutuman mai shekaru 48 dan kasar ta Jamus ya kutsa a guje da mota kan wasu mutane da ke zaune wajen wani wujen shakatawa da shan gahawa na bakin wani titin na birnin na Münster inda ya halaka mutanen biyu mace da namiji masu kana ya bindige kansa daga bisani.