Jamus: CDU ta lashe zabe a jihar Saarland | Labarai | DW | 26.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: CDU ta lashe zabe a jihar Saarland

Jam'iyar Christian Democrats (CDU) ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu nasara a zaben da aka gudanar a jihar Saarland da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Magoya bayan jam'iyyar CDU a Jamus na murnar lashe zabe a jihar Saarland

Magoya bayan jam'iyyar CDU a Jamus na murnar lashe zabe a jihar Saarland

Rahotanni sun nunar da cewa jam'iyyar ta CDU nada sama da kaso 40 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da abokiyar hamayyarta ta Social Democrat (SPD) ke da sama da kaso 30 cikin 100 na kuri'un. Wannan dai na nuni da cewa akwai sauran aiki gagarumi a gaban jam'iyyar ta SPD, a fatan da take da shi na lashe zaben shugabancin gwamnati a Jamus din, bayan da ta tsayar da Martin Schulz a matsayin dan takararta da zai kalubalanci Merkel a zaben da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa a kasar.