1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: CDU na dab da kafa kawance

Gazali Abdou Tasawa
October 25, 2017

Jam'iyyar CDU mai mulki a Jamus da takwarorinta na CSU da FDP da kuma ta The Greens da ke shirin kulla kawancen kafa gwamnati sun cimma matsaya kan wasu batutuwa.

https://p.dw.com/p/2mRxA
Deutschland Bundeskanzlerin Angela Merkel bei der Sitzung der Bundestagsfraktion von CDU und CSU in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Jam'iyyar CDU mai mulki a Jamus da takwarorinta na CSU da FDP da kuma ta The Greens da ke shirin kulla kawance da ake yi wa lakabin kawancan Jamaika da nufin kafa sabuwar gwamnati sun cimma matsaya kan jerin wasu matakai guda bakwai na rage karfin haraji da kuma yawan bashin da kasar ke ciyowa. 

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a karshen zagayen farko na zaman tattaunawarsu wacce kamfanin dillancin labaran na DPA ya ruwaito jam'iyyun  sun bayyana bukatar ganin wadannan sabbin matakai da suka cimma matsaya a kansu sun taimaka ga inganta rayuwar iyalai masu 'ya'ya da sauran masu samun karamin albashi a kasar ta Jamus, kazalika da gina gidajen haya dama gyaran tsaffin wadanda ke da akwai.