1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ba zata canza manufarta akan aikin sake gina Afghanistan ba

Ministan harkokin wajen Jamus F.-W. Steinmeier ya ce gwamnatin Jamus ba ta da wani shirin canza aikin samar da zaman lafiya da take yi a Afghanistan inda ta girke sojojin ta a arewacin kasar inda ke da dan kwanciyar hankali. Kalaman na mista Steinmeier ya biyo bayan wani taro ne da yayi da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jaap de Hoop Scheffer a birnin Berlin. Amirka da wasu kasashe membobin NATO na kira ga Jamus da ta girke sojoji a kudancin Afghanistan don hada karfi da sojojin da Amirka kewa jagora a yankin wajen yaki da ´yan tawayen Taliban. Mista Scheffer ya musanta cewa NATO na matsawa Jamus lamba da ta tura dakaru kudancin Afghanistan to amma ya ce kwamandojin NATO ba sa son a kayyade yawan sojojin da Jamus zata girke.