Jamus: An zargi wani da zama dan Boko Haram
January 26, 2018Talla
Mutumin dan shekaru 27 ya shiga hannun jami'an tsaro ne a ranar Larabar da ta gabata a yankin Bavaria, bincike ya nuna cewa ya na daya daga cikin mayakan kungiyar da suka taba kai hari a wata makaranta da wani kauye dama yin garkuwa da mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Bisa ga bayanan da aka bada, Amaechi Fred ya zama mamba na kungiyar a shekarar 2013 ya kuma amince da hannu a wasu hare-hare hudu da mayakan suka kaddamar kan farraren hula a tsawon shekara guda da ya yi a karkashin kungiyar. An shigar da kara don soma gudanar da shari'a kan mutumin.