Jamus: An kama wani da sayar da makamai ga dan bindiga
August 16, 2016Talla
Masu gabatar da kara sun ce mutumin Bajamushe ne mai shekaru 31 an kamashi ne a yammacin birnin Marburg. Dan bindigar wanda ya bude wuta da wata karamar bindiga samfurin Glock 17 a ranar 22 ga watan Yuli inda ya kashe mutane tara ya kuma jikkata wasu da dama kafin daga bisani ya kashe kansa. An yi imanin ya sayi bindigar ce a wata kasuwar bayan fage ta Internet da bata garin mutane