1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Amincewar jam'iyyu da gwamnati.

YAHAYA AHMEDNovember 14, 2005

Manyan jam'iyyun da za su kafa gwamnatin tarayya, sun amince da yarjejeniyar da kusoshinsu suka cim ma, bayan shawarwarin da suka shafe kusan maklwanni 8 suna yi.

https://p.dw.com/p/Bu4A
Wasu kusoshin jam'iyyar CDU
Wasu kusoshin jam'iyyar CDUHoto: AP

A karo na biyu a tarihin Jamus, an sami gwamnatin hadin gwiwa ta manyan jam’iyyun kasar, wato CDU da SPD. Hakan dai ya zo ne bayan wata doguwar tattaunawar da jam’iyyun biyu suka shafe makwanni 8 suna ta yi, wato dab da kammala zaben majalisar dokokin da aka gudanar a ran 18 ga watan Satumban da ya gabata. A tarukan da `yan jam’iyyun suka gudanar yau a biranen Berlin da Karlsruhe, sun yi amanna da yaejejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa da shugabanninsu suka cim ma. Hakan kuma, ya share fagen zaban Angela Merkel ke nan, tamkar farkon mace, wadda za ta shugabanci gwamnatin tarayya a tarihin Jamus. Har ila yau dai, `yan jam’iyyr SPD ma sun amince da Franz Müntefering tamkar mataimakin shugaban gwamnatin. A taron da suka yi a birnin Munich, `yan jam’iyyar CSU ta Baveriya, su ma sun amince da yarjejeniyar da aka cim ma.

Da take yi wa taron `yan jam’iyyarta jawabi a birnin Berlin, shugaban gwamnatin tarayya mai jiran gado, Angela Merkel, ta yi watsi da zargin da ake yi mata, na rashin kare maslahar jam’iyyar ta CDU, a tattaunawar kafa gwamnatin hadin gwiwar da kusoshin jam’iyyar suka yi da jam’iyyar SPD. Ta ce kamata ya yi dai, a bai wa sabuwar gwamnatin damar fara aikinta, a kuma ga irin kamun ludayin da za ta yi tukuna, kafin a fara zarginta.

Duk da zargin da `yan jam’iyyar wsuka yi mata dai, wakilai dari da 13 ne suka amince da yarjejeniyar, sa’annan guda 3 kuma suka nuna adawarsu da shrin.

A birnin Karlsruhe, inda jam’iyyar SPD ta gudanad da nata taron, mafi yawan `yan jam’iyyar ne suka ka da kuri’un amincewa da yarjejeniyar. Sun kuma yi amanna da nada `yan jam’iyyar guda 8 a mukamin m inistocin tarayya. Da yake yi wa taron jawabi, shugaban jam’iyyar ta SPD, Franz Müntefering, wanda shi ne zai zamo mataimakin shugaban gwamnatin tarayya da kuma ministan kwadago na tarayya, ya bayyana cewa, yarjejeniyar da aka cim man dai, ita ce ta fi fa’ida ga Jamus a halin yanzu. Bugu da kari kuma, mafi yawan ababan da aka yarje a kansu, sun kunshi manufofi ne da jam’iyyar SPDin ke bi. Ya kara da cewa:-

„Sabuwar gwamnatin dai sai ta fara aiki ne za a iya yanke hukunci a kanta. Babu abin da za a iya cewa game da ita a halin yanzu… Kamata ya yi, a nuna kwazo da bajinta, wajen huskantar kalubalen da ake ta fama da shi a nan Jamus a halin yanzu.“

A nasa bangaren kuma, shugaban gwamnatin tarayya mai barin gado, Gerhard Schröder, ya yi jawabin da ake gani kamar na ban kwana ne ga `yan jam’iyyar, inda ya yabi irin aikin da gwamnatinsa ta gudanar a taswon lokacin mulkinsa na shekaru 7. Amma ya kuma yi kakkausar suka ga wasu kafofin yada labarai, wadanda yake zargi da gindaya wa jam’iyyarsa shinge a lokacin yakin neman zabe. Ya dai yi kira ga `yan jam’iyyarsa da su yi taka tsantsan nan gaba, inda kuma ya ba su shawarar cewa:-

„Akwai mutane da yawa, wadanda ba su da wata sha’awa sai dai ganin an ta da zaune tsaye. Nan gaba ma, wannan halin ba zai ja da baya ba. Sai dai ka da ku bari ko mene ne ma ya ja hankalinku daga abin da kuka sanya a gaba. Ku kuma yi hankali a duk irin tattaunawar da za ku shiga inda za a yi muhawara kan tsarin dimukradiyya. Saboda irin wadannan tarukan, ba sa bunkasa tafarkin na dimukradiyya, sai ma kara raunana shi suke yi. Shi ya sa a gare ku duk na ke kira, ku kauce daga ire-iren wadannan, ba sa janyo wani abin alheri.“

Duk da cewa dai, `yan jam’iyyar SPDin sun amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwar, da yawa daga cikisnu na gunagnai ne kan karin harajin da za a yi a shekara 2007.