1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

JAMMIYYAR NNP TA HADE DA ANC MAI MULKI A AFRIKA TA KUDU.

Juyin juya halin siyasa a kasar Afrika ta kudu.

Jammiyar ANC mai Mulki.

Jammiyar ANC mai Mulki.

Rikicin siyasa ya barke a kasar Afrika ta kudu ,bayan tsohuwar jammiyar nuna wariyar launin fata ta sanar da rushewa a karshen mako,kusan karni guda da kirkiro ta domin inganta mulkin fararen fata.

Shugaban Jammiyar New National Party watau NNP a takaice Marthinus van Schalkwyk,ya sanar da hadewan jammiyar tasu da jammiya ANC ,da suka jima suna gwabzawa da juna.Sanar da rushe wannan jammiya na nufin kawo karshen kawo karshen jammiyar nuna wariyar launin fatan,wadda aka kafata a shekarata 1914 ,a matsayin jammiyar Kasa,watau National Party,kana ta mulki wannan kasa natsawon shekaru 40,kafin a shekarata ta 1994,da jammiyar ANC mai mulkin ta doketa,a karo na farko da akayi zaben jammiyyu da dama a kasar ta Afrika ta kudu.

Shugaban rusasshiyar jammiyar yayi kira ga sauran magoya bayanta dasu hade da jammiyar ANC,wadda jammiyar AN ta haramta a shekarata 1960,wadda kuma ta dau makamai ,shekara guda bayan nan domin yakan fararen fata marasa rinjaye.

To sai dai sauran jammiyyun adawa sun tofa albarkacin bakinsu,inda suke kira ga membobin jammiyar NNP din,wadda zata rushe baki daya a watan satumban shekara mai zuwa ,dacewa su hade da jammiyyun nasu.Shugaban jammiyar adawa Tony Leon,yace kasar Afrika ta kudu a yanzu tana fuskantar kalubale tsakanin jammiyar ANC da Democratic Alliance DA.Yace a wannan yanayi kowace kuria nada muhimmanci.

A yanzu haka dai kananan jammiyyun adawa na cigaba da zawarance wajen membobin rushasshiyar jammiyar dasu hade dasu.Ita kuwa shugabar jammiyar Independents Democrats Patricia de Lille cewa tayi,hadewar jammiyyar NNP da ANC ,babban kuskure.Domin inji ta ba sai jammiyu sun hade da ANC ne zasu iya mahawara kann makomar kasar Afrika ta kudu a siyasance ba.

Duk dacewa Shugaba Thabo Mbeki yayi maraba da wannan yunkuri na rusasshiyar jammiyar,har yanzu ana zargin shugaban rusasshiyar Jammiyar ta sayar da jammiyarsa ,domin samun mukamin gwamnati.

Jaridun kasar na cigaba da rubuta rahotannin dangane irin mukaman da gwamnatin Mbeki zata iya bashi.Alal misali jaridar Afrikans cewa tayi zaa iya bawa Mr Van mukamin ministan muhalli da harkoki na yawon shakatawa.

Wannan yunkuri NNP dai bazai kasa nasaba da koma baya da jammiyar ta samu a zaben daya gudana a watan Afrilu ba,inda ta samu kasa da kashi 2 cikin 100 na yawan kuriu da aka kada.Jammiyar National Party dai tayi mulki a Afrika ta kudu na tsawon shekaru 46,inda ta nuna wariyar alumma,ta kafa dokokin kasa dake musgunawa bakaken fata masu rinjaye a wannan kasa.A karshen wannan mulki ne a shekarata 1994,jammiyyar ta sauya Sunanta zuwa New National Party,NNP.Wannan yanayi da jammiyar ta kasance ciki na mai zama tarihi a kasar Afrika ta kudu,jammiyar da shugabanninta suka jefa Nelson Mandela a kurkuku,tare da watsi da Jammiyyar ANC daga harkokin siyasan wannan kasa,baya ga haramta mata gudanar da harkoki.

Zainab Mohammed.

 • Kwanan wata 12.08.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhL
 • Kwanan wata 12.08.2004
 • Mawallafi Zainab Mohammed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhL