Jammeh ya lashe zaben shugaban kasar Gambia da gagarumin rinjaye | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jammeh ya lashe zaben shugaban kasar Gambia da gagarumin rinjaye

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh, wanda ya haye kan karagar mulki a wani juyin mulki da ya yi shekaru 12 da suka wuce, ya sake lashe zaben shugaban kasar da gagarumin rinjaye. Sakamakon karshe da hukumar zaben ta bayar dazu dazun nan a birnin Banjul, ya nunar da shugaba Jammeh ne ya yi nasara a wannan zabe, wanda rahotanni suka ce mutane ba su fita sosai don kada kuri´a ba. shugaba Jammeh ya samu da yawa daga cikin kuri´un da aka kada na mazabu 47 daga 48 a zaben na jiya juma´a. Tun da farko dai an yi hasashen cewa shugaban mai shekaru 41 a duniya zai lashe zaben, wanda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce ba a kamanta dokoki na demukiradiya a ciki ba saboda tursasawa ´yan jarida da ´yan adawa.