Jammeh ya fara gudun hijira a kasar Equatorial Guinea | Labarai | DW | 22.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jammeh ya fara gudun hijira a kasar Equatorial Guinea

Tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya fice daga kasar da ya yi mulki na tsawon shekaru 22, a wani mataki na warware rikicin siyasa da kasar ta yammacin Afirka ta tsinci kanta a ciki.

Mutumin da tun farko ya ki sauka daga mulki duk da kaye da ya sha a zaben ranar 1 ga watan Disamba, Jammeh ya yi sanadiyyar tayar da jijiyar wuya da yunkurin daukar matakin soja, da nufin tilasta shi bawa sabon shugaban kasar Adama Barrow madafan iko.

Tsohon shugaban na Gambiya tare da rakiyar Shugaba Alpha Conde na Guinea sun bar birnin Banjul a wani karamin jirgin sama zuwa Conakry babban birnin Guinea kana daga bisani ya shige kasar Equatorial Guinea, inda zai yi zaman gudun hijira, a cewar shugaban kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza a birnin Dakar.