1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyun gwamnatin tarayyar Jamus da tsarin dokoki.

YAHAYA AHMEDJune 29, 2006

Wata barazanar ɓaraka na niyyar kunno kai tsakanin jam'iyyun SPD da na CDU a nan Jamus, waɗanda su ne suka kafa gwamnatin tarayya. Ana samun banbancin ra'ayi tsakanin jam'iyyun a kan batun zartad da dokokin yi wa kafofin tarayya garambawul da na haramta wariya a nan Jamus.

https://p.dw.com/p/BtzY
Shugabar gwamnatin tarayya Angela Merkel, a majalisar dokoki ta Bundestag.
Shugabar gwamnatin tarayya Angela Merkel, a majalisar dokoki ta Bundestag.Hoto: AP

Jam’iyyun CDU da na SPD, waɗanda su ne suka kafa gwamnatin haɗin gwiwa ta tarayya da ke ci yanzu a nan Jamus, sun fara wata muhawara mai tsanani, don warware rikicin bambancin ra’ayoyi tsakaninsu, wanda ke barazanar janyo musu ɓaraka. Akwai dai muhimman jigogi guda biyu, waɗanda majalisar dokokin tarayya za ta tattauna a kansu, kafin a ka da ƙuri’ar zartad da ƙuduri. Waɗannan jigogin kuwa, su ne btaun yi wa kafofin tarayya da na jihohi garambawul da kuma zartad da dokar nan ta haramta wariya a duk sassan halin rayuwa a nan Jamus. Tun da daɗewa ne dai ƙungiyar EU ta bukaci duk ƙasashe mambobinta da su zartad da wannan dokar, wato ta haramta wariya. Tsohuwar gwamnatin tarayya, ƙarƙashin Gerhard Schröder, ta yi ƙoƙarin shigad da dokar a majalisa. Amma, saboda zaɓen da aka gudanar kafin wa’adin gwamnatin ya cika, kundin bai sami bitar ’yan majalisar ba, balantana ma a ka da ƙuri’u a kanta. A lokacin yaƙin neman zaɓe kuma, ’yar takarar jam’iyyar CDU Angela Merkel, ta yi kakkausar suka ne ga dokar da kwatanta ta da wata mummunar dodanniya mai rusa duk wani yunƙuri da ake yi na samad da guraban aiki. Amma sai ga shi da ta hau karagar mulki, ita ce kuma ke neman a zartad da dokar ba tare da yi mata kwaskwarima ba. A nan dai, abokan ƙawancen gwamnatinta, daga jam’iyyar SPD sun nuna rashin jin daɗinsu. A jam’iyyar ta CDU ma, akwai waɗanda suka ƙi amincewa da tsarin dokar kamar yadda yake a halin yanzu. Duk da hakan dai, Volker Kauder, shugaban reshen jam’iyyun CDU da CSU a majalisar dokoki, ya ce ’yan majalisan za su amince da shirin:-

„Mun sami amincewar mafi yawan ’yan majalisarmu. Ban da takwarorinmu guda 6, duk sauran sun yarje su ka da kuri’ar amincewa da sabuwar dokar ta haramta wariya.“

To me ake son cim ma ne takamaimai da wannan dokar? Nauyi dai ya rataya a wuyar Jamus, da ta aiwatad da tsarin nan da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta gabatar na haramta duk wani mataki da zai nuna alamun wariya ga jama’a, saboda asalinsu, ko jinsinsu, ko kuma ƙabilarsu. Bugu da ƙari kuma, tsarin na EU na bukatar a haramta duk wani salo da zai zalunci wani nau’i na jama’a kamar naƙasassu, ko tsoffin mutane, ko ’yan luwaɗu, ko mabiya wani addini ko kuma masu hangen duniya da ra’ayi daban.

To a nan ma dai, ra’ayoyin jam’iyyun gwamnatin haɗin gwiwar sun bambanta. Saboda kamfanoni, masu bin tafarkin jari hujja, na ganin cewa idan an zartad da dokar, to za a sami ambaliyar ƙararraki a kotuna, saboda mutane da yawa za su ga an ƙi ɗaukarsu aiki ne saboda wariya, ko kuma saboda wata alama ta bambancinsu da sauran jama’a ne aka hana su gidajen haya, da dai sauransu. Game da hakan ne dai, gwamnonin jihohin tarayya na jam’iyyar CDU suka bukaci majalisar dattijai, wato Bundesrat, ta yi wa shirin dokar canje-canje. Jam’iyyun ƙawancen dai sun yi wani taron gaggawa don warware rashin jituwar da ake ta ƙara samu tsakaninsu.

A kan batun yi wa tsarin kafofin tarayya da na jihohi kwaskwarima kuma, ’yan jam’iyyar SPD sun yi barazanar yi wa shirin babakere, idan jam’iyyar CDU ba ta janye wasu bukatunta ba. Kamar dai yadda shugaban reshen jam’iyyar SPDin a majalisar dokoki, Peter Struck ya bayyanar:-

„Reshen jam’iyyar SPD a majalisa, bayan wata doguwar muhawarar da ta yi, kan batun yi wa kafofin tarayya a nan Jamus garambawul, ta tsai da wata shawara. Mafi yawan mambobinta ne suka yarje da amincewa da tsarin, bayan shawarwarin da muka yi da abokan haɗin gwiwar.“

Wato a nan dai, za a iya cewa ƙusoshin jam’iyyun biyu sun ƙago wani salo ne na soke abin da bai dace da ra’ayoyinsu ba a dokokin da ake niyyar zartarwa – waɗanda suka ƙunshi dokar haramta wariya da dokar yi wa kafofin tarayya garambawul. Sai dai can ƙasa, mambobin jam’iyyun na nan na ta ce-ce ku- ce a kan waɗannan batutuwan.