1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyun adawa a Turkiyya sun yi hadaka

Zulaiha Abubakar
May 5, 2018

Manyan jam'iyyun adawa hudu a kasar Turkiyya sun sanar da dunkulewa guri daya don karawa da jam'iyyar shugaban kasar Receep Tayyib Erdogan a zaben kasar mai zuwa cikin watan Yuni.

https://p.dw.com/p/2xFBn
 Receep Tayyib Erdogan
Receep Tayyib ErdoganHoto: Reuters/M. Cetinmuhurdar

Hadakar jam'iyyun mai suna Nation Alliance ta rabawa manema labarai wannan sanarwa ce a yau Asabar jim kadan bayan cimma yarjejeniya tsakaninsu, sanarwar ta kara da cewar wannan shine matakin da zasu dauka don ganin kasar ta rabauta da sabon shugaban kasa.

Tun da fari jam'iyya mai mulki ta shugaba Erdorgan ta hade da wa su manyan jam'iyyu biyu a kasar inda suka yiwa kundin tsarin milkin kasar wata kwaskwarima da ta karawa shugaban kasar karfin iko, lamarin dake cigaba da samun suka daga bangarori daban daban.

Shugaba Erdogan dai ya bukaci gudanar da zabubbukan kasar shekara guda gabanin wa'adi.