Jam´iyyar MDC a Zimbabwe zata shiga zabe amma... | Labarai | DW | 29.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyyar MDC a Zimbabwe zata shiga zabe amma...

Shugaban adawa na Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, yace tsayawar jam´iyyar su takara, a zabe na gaba ya danganta ne da tattaunawar da jam´iyyar take ne da shugaba Mugabe. Mr Tsvangirai ya fadi hakan ne yau a Harare a wani taron gaggami na cikar jam´iyyar ta MDC shekaru takwas da kafuwa.Morgan Tsvangirai, wanda ke zagaye da magoya bayan sa, ya kara da cewa,dole ne shugaba Mugabe ya dakatar da cin zarafin yan adawa, don basu damar yin zabe a yanayi mai tsabta. Gudanar da zabe mai tsafta da adaklci inji Tsvangirai shine,burin da jam´iyyar tasu ta MDC tasa a gaba. A dai shekara mai kamawa ne ake sa ran gudanar da zaben gama gari a kasar, wanda shugaba Robert Mugabe ke takara na sake neman shugabancin kasar.