Jam´iyyar masu sassauci a Canada tasha kaye | Labarai | DW | 24.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyyar masu sassauci a Canada tasha kaye

Jam´iyyar masu sassauci ta kasar Canada karkashin shugaba Paul Martin ta amince da kayen data sha a hannun jam´iyyar masu ra´ayi irin ta mazan jiya.

Rahotanni dai daga kasar na nuni da cewa, wannan nasara ta jam´iyyar yan mazan jiyan karkashin Stephen Harper, ya kawo karshen mulkin jam´iyyar ta masu sassauci, data shafe shekaru 12 a gadon mulkin kasar.

Wannan dai zabe na gama gari ya kasance irin sa na biyu a tsawon watanni 18 da suka gabata. Jam´iyyar adawa ta kasar ta bukaci gudanar da wannan zaben ne a watan nuwambar bara, bayan data zargi gwamnatin Paul Martins da daurewa cin hanci da rashawa gindi.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labarai sun rawaito faraminista Paul Martins na fadin cewa zai yi murabus daga shugabancin jam´iyyar su ta masu sassaucin.