Jamiyyar Kadima ta Sharom taja daga
January 16, 2006Talla
Sabuwar Jamiyyar Mr Sharon, wato Kadima ta nada Mr Ehud Olmert a matsayin shugabanta na riko da zai jagorance ta a lokacin zaben gama garri da aka shirya yi a ranar 28 ga watan maris na wannan shekara da muke ciki.
A cewar wata sanarwa data fito daga jamiyyar ta Kadima, ta tabbatar da cewa daukar wannan mataki ya biyo bayan irin halin da yake ciki ne a yanzu na matsananciyar rashin lafiya.
Idan dai an tuna Faraminista Ariel Sharon ya tsinci kann sa ne a cikin wannan hali bayan ya fuskanci mummunan bugun zujiya, data haifar masa da tiyata a cikin kwakwalwarsa.
Ya zuwa yanzu dai bayanai sun nunar da cewa har yanzu Mr Sharon na cikin dogon hali na suma, wanda likitoci suce ci gaba da kasancewa a wannan hali hatsari ne ga rayuwar faraministan.