Jam′iyyar CDU ta gudanar taro | Labarai | DW | 19.07.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar CDU ta gudanar taro

Gwamnatin Jamus ta ce za ta iya ci gaba da mulki

default

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel.

Gwamnatin gamin gambiza ta Angela Merkel da ke mulkin Jamus ta yi ƙoƙarin ba al'umar tabbacin cewa har ila yau tana da ƙarfin tafiyar da mulki duk da murabus na gwamnan jihar Hamburg da ke zaman irinsa na shida da ta fuskanta a wannan shekara. Bisa ga dukkan alamu gwamnatin tana fuskantar janyewar gaggan shugabanninta da suka haɗa da magajin garin na Hamburg mai cike da farin jini, wato Ole von Beust.

Murabus ɗin von Beust na zaman irinsa na shida da gwamnatin ta fuskanta tun daga watan Satumban bara. A wani taro da jam'iyyar CDU ta yi a yau Litinin 'yan siyasarta sun yi watsi da abin da ya faru tare da lasan takobin samar da sabbin ƙwararru. A dai halin yanzu matsayin yardar da al'uma suka bai wa Merkel yayi ƙasa zuwa kashi 35 daga cikin ɗari.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 19.07.2010
 • Mawallafi Halimatu Abbas
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/OPRL
 • Kwanan wata 19.07.2010
 • Mawallafi Halimatu Abbas
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/OPRL