Jami′yun Jamus shida sun kara a muhawara | Labarai | DW | 14.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'yun Jamus shida sun kara a muhawara

Ana kasa da mokonni biyu a gudanar da babban zabe, wakilan manyan jam'iyun siyasan kasar Jamus sun fafata a cikin shirin muhawarar DW Conflict Zone.

Yadda za'a tinkari tsare-tsaren harkokin waje da kalubalen da ke gaban sabo ko sabuwar shugabar gwamnati da za a zaba, ya dauki hankalin muhawarar, kazalika tattaunawar ta yi zafi kan batutuwa da suka hada da neman mafita ga rikicin Koriya ta Arewa da kuma batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai EU da matsalar bakin haure da batun tinkarar tsamin dangantaka tsakanin Jamus da Turkiya.

Wakilan jam'iyu shida daga jam'iyar CDU ta 'yan masu ra'ayin rikau da SPD da jamiyyar 'yan Liberal masu sassauci ta FDP da kuma jam'iyar AFD masu kin baki da kuma jam'iyar masu kare muhali ta Green da 'yan guruguzu watau LINK  . Muhawarar dai ta dau zafi ne bayan da aka rika jifa tambayoyi daga shafukan sada zumunta.