1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam´iyun Jamus a zaɓen majalisar Turai

A ranar 7 ga watannan na Yuni al´ummomin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai za su kaɗa ƙuri´a don zaɓan sabuwar majalisar dokoki.

default

Ginin majalisar Turai

A nan Jamus kuwa wannan zaɓen na zama wata manuniya ga jam´iyun siyasar ƙasar a dangane da zaɓen ´yan majalisar dokoki da zai gudana a cikin watan Satumba mai zuwa. Yayin da wasunsu ke fata zaɓen na Turai zai musu kyakkyawar shimfiɗa gabanin zaɓen na cikin gida, wasunsu kuwa fargaba suke yi na samun koma-baya.

Matsalar ƙarancin masu kaɗa ƙuri´a a zaɓen ´yan majalisar dokokin Turai ta fi shafan manyan jam´iyu. Yawan masu kaɗa ƙuri´ar ya ragu tun bayan zaɓen farko a 1979 daga kashi 65.7 cikin 100 zuwa kashi 43 cikin 100 a shekara ta 2004. Adadin na iya raguwa a wannan karo. Ɗaukacin al´ummomi dai ba sa ɗaukar majalisar ta Turai da wani muhimmanci. Alal misali a nan Jamus idan wani bai gamsu da aikin jam´iyarsa a cikin gida ba, to ba ya fita kaɗa ƙuri´a a zaɓen na Turai. A dangane da haka Angela Merkel dake jagorantar gwamnatin ƙawance tsakanin CDU da CSU da SPD ta yi kira da a fita kaɗa ƙuri´a.

"Muna fata mutane za su fita kaɗa ƙuri´a, a cikin lokacin da ya saura na yaƙin neman zaɓe muna ƙoƙarin jawo hankalin jama´a domin su san muhimmanci aikin majalisar Turai a garemu, saboda haka ya kamata mu samu gagarumin wakilci a cikin majalisar."

A lokacin zaɓen ´yan majalisar dokokin Turai da ya gudana a shekarar 2004, jam´iyar SPD da The Greens ke kan mulki a nan Jamus, inda a lokacin farin jinin gwamnatin Gerhard Schröder ya ragu matuƙa. A saboda haka ta rasa magoya baya ga jam´iyar PDS wadda yanzu ta rikiɗe ta zama ta masu neman sauyi. Wasunsu su yi zamansu a gida ba su tafi kaɗa ƙuri´a ba. A yau wannan na zaman wata fa´ida. Kashi 21.5 cikin 100 a wancan lokaci babban koma-baya ne, yanzu SPD na fatan abubuwa za su canza. Babban sakatarenta Hubertus Heil ya yi nuni da cewa jam´iyar SPD na amfani da matsalolin tattalin arziki da ake fama da su inda take nesanta kanta da abokiyar ƙawancenta a cikin gwamnatin Berlin.

"Jam´iyun CDU da CSU suna fifita harkokin kasuwanci akan al´ummomin nahiyar Turai. Suna son a yi amfani da tsarin jari hujja tsantsa a Turai. Amma mu ´yan Social democrats muna da ra´ayin cewa dole a sanya bil Adama kan gaba, saboda haka muke goyon bayan kyakkyawan tsarin zamantakewa a Turai."

Ita ma jam´iyar The Greens wadda SPD ta fi ƙaunar yin ƙawance da ita na da irin ra´ayin SPD. A yaƙin neman zaɓe na ´yan majalisar Turai, babban ɗan takararta a zaɓen Jürgen Trittin cewa ya yi.

"Jam´iyun CDU da CSU sun rasa alƙibla a Turai. Sannu a hankali suna rusa tsarin taimakawa jama´a. Martaninmu a nan shi ne, muna son ƙarin haɗin kan Turai domin a tabbatar da kyakkyawan tsarin zamantakewa."

To sai dai a nata ɓangare jam´iyar masu neman sauyi ba zata yarda SPD da The Greens sun yi amfani da manufarta don samun ƙuri´un jama´a ba. Shugabanta Lothar Bisky ya yi tuni da lokacin gwamnatin haɗin guiwa tsakanin SPD da The Greens inda suka hana aiwatar da tsarin albashi mafi ƙanƙanta a Jamus abin da ya saɓa da manufar Turai. Ganin yadda sauran jam´iyun ke lalube cikin duhu dangane da matsalar tattalin arziki, fata ake cewa jam´iyar FDP ta masu sassaucin ra´ayi za ta ci gajiyar asarar ƙuiri´un da waɗannan jam´iyu za su yi.

Mawallafa: Peter Stützle/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed