Jam´iyun adawa a Tchad sun hiddo sanarwa a game da rikicin ƙasar | Labarai | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyun adawa a Tchad sun hiddo sanarwa a game da rikicin ƙasar

Jam´iyun adawa a ƙasar Tchad, sun bayyana matsayin su, a gmeda rikicin da ke wakana, tsakain yan tawaye, da dakarun gwamnati.

Sanarwar da haɗin gwiwar yan adawa su ka fiddo, a yau alhamis, ta buƙaci shugaba Idriss Deby Itno, ya fasa shirya zaɓen shugaban ƙasa, da za a yi ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa, sannan ya hau tebrin shawara, da yan adawa, domin samar da sabin hanyoyin shirya zaɓe cikin tsabta da fahintar juna.

A ɗaya wajen kakakin yan adawar Tchad, Ibn Umar Mahamat saleh, ya yi Allah wadai da rawar da ƙasar France ta taka, cikin wannan rikici.

Ya ce maimakon France, ta ɗauki matakan sasanta ɓangarorin 2, kamar irin na Cote D´Ivoire, sai ta nuna fifiko ga gwammnati.

Duk da haka, kakakin yan dawar, ya yi kira ga gwamnatin France da ta sake lale muddun ta na bukatar kwancviyar hankali mai ɗorewa a ƙasar Tchad.

A ɓangaren yan tawaye, suma, sun zargi ƙasar France da ɗaurewa Idriis Deby gindi, bayan da ministan harakokin wajen ƙasar Phillipes Dutse Blazy, yayi wasti da bukatar yan tawaye, ta haɗuwa da shi.

A halin da ake ciki kuma, jami´an tsaro, na ci gaba da kame kamen jama´a, a birnin NjDjamena, da sauramn biranen ƙasar, da ake zargi da hannu a cikin tawaye.

Ƙungiyar kare haƙoƙin bani adama, ta ƙasa, ta yi Allah wadai da wannan kame, na kan mai uwa da wabi.