Jam´iyar ´yan adawa a Taiwan ta doshi hanyar lashe zaben kananan hukumomi | Labarai | DW | 03.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar ´yan adawa a Taiwan ta doshi hanyar lashe zaben kananan hukumomi

Babbar jam´iyar `yan adawa ta masu kishin kasa a tsibirin Taiwan ta lashe mafi yawa daga cikin kujerun kananan hukumomi a zaben da aka gudanar yau asabar. Wannan nasarar zata ba shugaban jam´iyar Ma Ying-Jeou wani kwakwarar matsayi gabanin zaben shugaban kasa da za´a yi a shekara ta 2008. Bayan an kammala kidayar kashi 75 cikin 100 na kuri´un da aka kada, hukumar zaben kasar ta ce jam´iyar ´yan kishin kasa da kawayenta na gaba a mazabu 17 daga cikin 23 da ak yi takara cikinsu. Hukumar zaben ta ce jam´iyar Democratic Progressive wadda ke jan ragamar mulki ta na gaba a sauran mazabu 6. Kuri´ar ta yau dai na matsayin mizanin auna farin jinin shugaban masu kishin kasa Ma Ying-Jeou, wanda ake sa rai zai jagoranci ´yan adawa a zaben shugaban kasa a shekara ta 2008.