Jam´iyar SPD ta lashe zaɓe a Jihar Brême ta Jamus | Labarai | DW | 13.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar SPD ta lashe zaɓe a Jihar Brême ta Jamus

Jam´iyar SPD ta lashe zaɓen yan majalisun jihohi da ya gudana yau, a jihar Breme, da ke arewa maso yamacin ƙasar Jamus.

SPD ta samu galaba tare da kimanin kashi 38 bisa na yawan ƙuri´un da aka kaɗa, a yayin da CDU ta tashi da kashi 26 bisa 100.

Dukkan jam´iyun 2,sun samu rogowar ƙuri´u a wannan jiha, idan a ka kwatanta da zaɓukan da su ka wakana a baya.

Jam´iyar masu fafatakar kare mahhali ta The Greens, ta zo sahu na 3, tare da sakamako mai tsoka, da ba ta taɓa samu ba zaɓen baya.

Su ma haɗin gwiwar jama´iyu masu tsatsauran ra´ayin gurguzu, sun yi nasara shiga a karo na farko majalisar dokokin jihar, tare da kashi 8 bisa 100, na jimillar ƙuri´un.