1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar Republican ta sha kayi a zaɓen Amurika

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buck

Bayan rinjayen da ta samu a Majalisar wakilan Amurika, jama´iyar Democrate, ta kuma yi nasara a Majalisar dattawa.

Dann takara Jim Webb na Democrate ya kada abokin hamayar sa ,Georges Allen a Virginia, jihar da ta kasance tamkar raba gardama, tsakanin jam´iyun 2,bayan kunen dokin da su ka yi, a yawan kujeru a Majalisar dattawa.

Daga cikin jimillar kujeru 100, da wannan Majalisa ta ƙunsa, yan Democrate, sun samu 51.

A sakamakon wannan mumunan kayi, da shugaba Georges Bush ya sha, a majalisun guda 2, tun jiya ya bayyana amincewar sa, da murabus ɗin sakatarann tsaro Donald Rumsfeld, daga muƙamin sa.

Kamar yadda ya nunar a jawabin da yayi, shugaba Bush ya ce, mafi yawan Amurikawa sun kaɗa ƙuri´a, domin hidda takaicin yaƙin ƙasar Irak, wanda ya zuwa yanzu, ya hadasa mutuwar sojojin Amurika kussan dubu 3.

Wannan saban yanayi da Amurika ta shiga , ko shaka babu, zai kawo cenje-cenje, a fagen siyasa, da na diplomatiar dunia, inji manazarta al´ammura.