Jam′iyar PPP ta Pakistan ta sanar da sunan sabon shugabanta. | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyar PPP ta Pakistan ta sanar da sunan sabon shugabanta.

A ƙasar Pakistan, jam’iyar marigayiya Benezir Bhutto, ta naɗa ɗan marigayiyar da mijinta a matsayin shugaba da mataimaki. Bi-lawal Zardari mai shekaru 19 da haifuwa, zai ɗare kujerar shugaba, a yayin da mijinta Asif Ali Zardari zai rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyar ta PPP, kana da kula da harkokin jam’iyar har sai bayan Bi-lawal ya kammala karatunsa. Kisan Bhutto ya haifar da tashe-tashen hankulla, da kuma tababa kan yiwuwar zaben 8 ga watan janairu. Asif ya shaidawa jam’iyar ta PPP cewar Benezir Bhutto ta yanke shawarar naɗa Bilawal shugaba tun kafin ta koma gida Pakistan ranar sha takwas ga watan oktoban da ya gabata.