Jam´iyar PPP mai goyon bayan Thaksin ta lashe zaɓen ƙasar Thailand | Labarai | DW | 24.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar PPP mai goyon bayan Thaksin ta lashe zaɓen ƙasar Thailand

Ƙungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da zaɓen ´yan majalisar dokokin Thailand tana mai cewa wani gagarumin mataki ne wajen mayar ƙasar bisa turbar mulki da kundin tsarin mulkin kasa. Kasar Portugal dake shugabancin ƙungiyar EU a yanzu ta ce sakamakon zaben ya tabbatar da buƙatun al´ummomin Thailand na rungumar mulkin dimokuradiyya tare da daukar makomarsu a hannu. A zaben dai jam´iyar FM Thaksin wanda aka yiwa juyin mulki kimamnin watanni 15 da suka wuce, ta yi nasara da rinjaye. To sai dai bayan kammala ƙidayar kuri´u da aka kaƙa ƙiris ya ragewa jam´iyar ta PPP ta samu gagarumin rinjaye, inji hukumar zaɓe a birnin Bangkok. To sai dai ba a san irin martanin da rundunar sojoin ƙasar zata mayar ba.