Jamiyar PDP a Najeriya ta kori gwamnan jihar Bayelsa | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamiyar PDP a Najeriya ta kori gwamnan jihar Bayelsa

Jamiyar dake mulki ta shugaba Olusegun Obasanjo a Nijeria, ta kori gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamesiya wanda aka kama da laifin halatta kudin haram a kasar Burtaniya.

Gwamnan na Bayelsa ya tsere daga Burtaniya zuwa Najeria inda yake da kariya daga baiyana gaban kuliya.

Wata sanarwar jamiyar ta baiyana Alamesiya da cewa ya bata suna tare da mutuncin jamiyar.

A ranar 15 ga watan satumba ne mahukuntan Burtaniya suka kama gwamnan da kudaden da ya sato na gwamnati har dala miliyan 3 da dubu dari biyu.

Ya kuma baiyana a ofishinsa a ranar 21 ga watan nuwamba yana mai cewa Allah ne ya cece shi.