1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar Labour zata janye daga gabashin Birnin Kudus

January 21, 2006
https://p.dw.com/p/BvBL

Jam´iyar Labour a Isra´ila ta ce a shirye ta ke ta bar yankin larabawa dake gabashin Birnin Kudus da Isra´ila ta mayar karkashin ikonta, idan aka kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe da Falasdinawa. Hakan dai na kunshe ne a cikin manufofin jam´iyar ta Labour dangane da zaben ´yan majalisar dokokin Isra´ila da zai gudana a ranar 28 ga watan maris. Wannan dai shi ne karon farko da wata babbar jam´iyar Isra´ila ta nuna shirin janyewa daga yankin na gabashin Birnin Kudus. Babban jami´in sulhu na Falasdinawa Saeb Erekat yayi mraba da wannan yunkuri na jam´iyar ta Labour, wanda ya ce zai ba da damar warware rikicin kasashe biyu wanda zai kai ga samar da dawwamammen zaman lafiya.