Jam′iyar Berlusconi ta yi nasara a zaɓen jihohi | Labarai | DW | 30.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyar Berlusconi ta yi nasara a zaɓen jihohi

Jam'iyar Berlesconi ta yi bazata a zaɓen jihohi a ƙasar Italiya

default

Berlusconi na ƙaɗa ƙuria' a zaɓen 28 Mars 2010

Haɗin guywar jami'iyun da ke ƙawance da jam'iyar Silvio Berlusconi sun smu nasara a zaɓen lordina da aka gudanar a ƙasar Italiya a ranakun lahadi da litinin, da kashi 26,7 yayin da jam iyar adawar ke da kashi 25,9.

jam'iyun dai sun yi nasara kwace muhiman garuruwan da suka haɗa da birnin Rome da turin wanda a da suke cikin hannu jam'iyar yan adawa ta yan socialiste.

Yazu yanzu dai a cikin jihohi 20 da ake dasu yan adawar na riƙe da lordinan 7 kwai ,to amma kafin zaɓen sune ke riƙe da gundumom 11 bisa 13.

Tun da farko dai jam iyyar ta Berlusconi bata sa ran samun nasara a zaɓen da ta fi bada karfi ga yankunan Calabre da Campanie,

,wani kakakin gwamnatin Paolo Bonaiuti ya bayyana cewa wannan ba ƙaramar sa'ace ba. ga irin wannan zaɓuɓuka da al uma ke yin amfani da su domin baiwa gwamnati kashedi.

jam'iyar dai ta Berlusconi ta samu goyon bayan ne daga yanki arewacin ƙasar,inda yan takara Jamiyar ligue ta maikata ta yi nasara a yankin Piemont wace kuma take da kashi 12,7 na ƙuri'un da aka ƙaɗa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Abdullahi Tanko Bala