Jam´iyar ANPP a Nijeriya ta zabi Janar Buhari a matsayin dan takarar ta a zaben badi | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar ANPP a Nijeriya ta zabi Janar Buhari a matsayin dan takarar ta a zaben badi

Babbar jam´iyar adawa a tarayyar Nijeriya ANPP ta zabi tsohon shugaban gwamnatin mulkin soji Mohammad Buhari a matsayin dan takarar ta a zaben shugabancin Nijeriya da zai gudana a watan afrilun shekara ta 2007. Buharin ya samu nasarar lashe zaben na fid da gwanin ne bayan da sauran ´yan takara su 6 suka janye. Zaben sa a gun babban taron jam´iyar da ya gudana a birnin Abuja, ya zo ne kwana guda daya kacal bayan da jam´iyar da ke jan ragamar mulki a tarayyar ta Nijeriya wato PDP ta zabi gwamnan jihar Katsina Umaru Musa ´Yar´aduwa a matsayin dan takarar ta na zaben shugaban kasar da za´a yi a badi idan Allah Ya kai mu. Bayan an ba sakamakon zaben Buhari ya fadawa mahalarta taron cewa al´umar Nijeriya na bayan su saboda su ne da tsare tsare na gari wadanda zasu fid da Nijeriya daga wahalhalu iri daban daban da ta ke fuskanta.