Jamiyar adawa ta tasamma lashe zabukan majalisun jihohi 2 a Jamus
September 17, 2006Talla
Sakamakon wucin gadi na zaben yan majalisun dokoki da aka gudanar a jihohi 2 a nan Jamus,sun nuna cewa jamiyar shugabar gwamnati Angela Merkel tana a baya,yayinda jamiyar masu tsatsauran raayi ke kann gaba.
Jamiyar Christian Democrats ta Merkel tazo na biyu a zaben yan majalisun na jihohin Berlin da Mekelenburg Pomeraniya.