1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyar adawa a Kenya ta shirya gangami a mako mai zuwa

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/CoQD

Babbar jam’iyar adawa ta Kenya tana shirin gudanar da wani babban gangami na nuna adawa da sake zaɓen shugaba Mwai Kibaki. Wani mai magana da yawun jam’iyar ya faɗawa manema labarai a birnin Nairobi cewa gangamin wani maida martani ne ga rashin samun nasarar shiga tsakani na AU don sasanta rikicin. ‘Yan sanda a ƙasar dai sun dunƙufar da yunkuri na baya da ‘yan adawa sukayi na gudanar da gangamin. Wannan kira kuma ya zo sa’o’i kaɗan bayan tsohon sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya amince ya jagoranci tawagar masu shiga tsakani na Afurka a kokarin baya bayan nan na kawo ƙarshen rikicin. Shugaban adawa Raila Odinga da magoya bayansa suna zargin Kibaki da yin magudin zaɓe .Akalla mutane 600 suka rasa rayukansu wasu kuma 250,000 suka bar gidajensu cikin rikicin da ya biyo bayan zaɓen ranar 27 ga watan Disamba.