Jam´iyar adawa a Kenya ta samu galaba a majalisar dokoki | Labarai | DW | 16.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyar adawa a Kenya ta samu galaba a majalisar dokoki

Jam´iyar adawa ta ƙasar Kenya ta samu wata nasara da ƙaramin rinjaye a zaman farko na majalisar dokoki tun bayan sake zaɓen shugaba Mwai Kibaki da ake taƙaddama akan sa. A wata ƙuri´a da aka kaɗa a majalisar ɗan takarar ´yan adawa Kenneth Marende ya yi nasara lashe zaɓen kakakin majalisar, muƙami mai matuƙar muhimmanci. A kuma halin da ake ciki ´yan adawa sun lashi takobin ci-gaba da gudanar da zanga-zangar kwanaki uku don ƙalubalantar sake zaɓen shugaba Kibaki. Daukacin ´yan ƙasar ta Kenya na fargabar cewa zanga-zangar wadda za a fara a yau laraba zata haddasa ƙarin tashe tashen hankula tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zangar. Fiye da mutane 600 aka kashe a tarzomar da ta biyo bayan bayyana sakamakon zaɓen wanda ya bawa shugaba Kibaki nasara.