Jamiyar adawa a Italiya tayi ikrarin lashe zabe | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamiyar adawa a Italiya tayi ikrarin lashe zabe

Jamiyar adawa ta Romano Prodi a kasar Italiya,tayi ikrarin cewa,ita ce ta samu nasara a zaben majalisar dokoki da aka gudanar a kasar.

Ana shi bangare Firaminista Silvio Berlusconi ya ja da wannan batu,yana mai kira da a sake kirga kuriun da aka kada.

Sakamakon baya bayan nan ya nuna cewa,jamiyar adawa ta lashe fiye da kashi 49 cikin dari na kuriu da aka kada na majalisar wakilai,yayinda a majalisar dattijai jamiyar Berlusconi dake mulki take kann gaba da karin kujera daya.

Masu lura da alamuran siyasa na kasar Italiya sunce dukkaninsu jamiyun basu da cikakken rinjaye da zai basu damar kafa gwamnati.