Jamiyar AC a Najeriya ta zabi Atiku | Labarai | DW | 21.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamiyar AC a Najeriya ta zabi Atiku

Jamiyar adawa ta Action Congress a Nijeriya ta zabi mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na 2007.

Atiku dan shekaru 60 da haihuwa an dakatar da shi daga jamiyar dake mulki ta PDP a watan satumba,kodayake baa san ko Atikun zai ci gaba da rike mukaminsa na mataimakin shugaban kasa ba.

Masu nazari dai sun baiyana tsoron cewa sauke Atiku daga wannan matsayi zai iya haddasa rikici game da kundin tsarin mulkin kasar.

Atiku da shugaba Obasanjo mai barin gado dai sun samu takun saka tsakaninsu bayan zargi da sukayiwa juma na cin hanci.