1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'iyyar Adawa da janye a Zimbabwe

Zainab MohammedJune 22, 2008

Martanin kasashen duniya akan halin da ake ciki a Zimbabwe

https://p.dw.com/p/EONl
Shugaban adawa a Zimbabawe, Morgan Tsvangir,Hoto: AP

Ƙasashen duniya na cigaba da kira dangane da ɗaukar tsauraran matakai na ladabtar da shugaba Robert Mugabe adangane da halin matsanancin rayuwa da kasar ke cigaba da kasancewa ci,a hannu guda da gallazawa 'yan adawa azaba a ɓangaren jami'an tsaro.

Magoya bayan jami'iyyar Zanu-Pf mai mulki kena ke cigaba da cin karensu babu babbaka a kasar ta Zimbabawe.ayayinda ya rage kasa da mako guda a je zagaye na biyun zaben shugaban kasa dai shugaban Adawa ta MDC Morgan Tsivandirai ya sanar da zartarwar jami'iyyarsa na janyewa .

Bayan wani zaman taro da magabatan MDC suka gudanar a birnin Harare,jami'iyyar ta ce zata janye daga zaɓen 27 ga wata ne saboda yadda ake cigaba da cin zarafin magoya bayanta,kana da gudun tabka magudi.

Ata bakin Tsvangirai,juma'a mai kyau daga laraba ake sani,saboda babu alamun yin adalci balle gaskiya a wannan zaben.

Shugaba Robert Mugabe a nashi bangaren dai yasha nanata cewar jami'iyyarsa ta Zanu-Pf bata taba faɗuwa zabe ba.

Shugabannin ƙasashen turai da sauran na ƙasashen duniya dai sun koka dangane da halin da al'ummomin kasar ta Zimbabwe ke ci,tare da ,kira ga Robert Mugabe daya dubi al'ummar tasa da idanun rahama.

Manazarta na ganin cewa halin da ake ciki yanzu da yadda ake gasawa 'yan adawa aya a han nu ba wani sabon abu bane a siyasar Zimbabwe,kamar yadda mai fafutukar kare hakkin jama'a Shari Eppel tayi nuni dashi...

"Abunda gwamnati takeyi a halin yanzu ba sabon abu bane,domin ana amfani da jamia'an tsaro wajen cin zarafin mutane,waɗanda su kansu ke cewar suna aiwatar da umurni na na robert Mugabe"

Rahotanni daga Zimbabwew dai na nuni dacewar daruruwan mutane ne ke cigaba da rasa rayukansu,mafi yawa ma ba a sani,baya ga mutane da dama dake ɓacewa,kana wasu a nakasa su.

Sakamakon rigingimu na siyasa da Zimbabwe ke ciki,tattalin arzikin ta ya durkushe,inda al'ummarta ke cigaba da rayuwa cikin hali mawuyaci sakamakon yunwa da fatara.Tsohon Primiyan Britaniya Tony Blair yayi Allah wadan halin da zimbabwe ke ciki...

"Halin takaici ne zimbabwe take ciki,kuma a bangaremmu na shugabannin duniya muna Allah wadan hare-jaremn da ake cigaba da kaiwa talakawa.."

Ita kuwa shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ,bayyana takaici tayi ta halin mawuyacin rayuwa da al'ummomin Zimbabwe ke cigaba da kasancewa ciki na lokaci mai tsawo......Adangane da hakane tayi kira ga kasashen dake makwabtaka da ita dasu taka rawa wajen ceto wannan kasa da a baya ta zame musu abun alfahari.

To amma a ganin mai shiga tsakani a rikicin siyara Zimbabwe,kuma shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki,abubuwa sun fara daidaita....

Da janyewar jami'iyyar adawa ta MDC daga zagaye na biyun zaɓen shugaban kasar dai, babu wanda ya san makomar siyasa a ƙasar ta Zimbabwe.