Jamiin Jamus da Iyalansa sun iso gida,bayan sace su a Yemen | Labarai | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamiin Jamus da Iyalansa sun iso gida,bayan sace su a Yemen

Tsohon jamiin diplomasiya na kasar jamus tare da iyalinsa a kasar sun iso gida,bayan an samu nasarar kwato su daga hannun wasu yan kabila da suka yi garkuwa da su a kasar Yemen.

Jürgen Chrobog tsohon jakada kuma tsohon mataimakin ministan harkokin wajen Jamus,sun iso birnin Koln tare da mai dakinsa da kuma yaransu biyu,cikin wani jirgi na musamman.

Chrobog ya fadawa manema labarai cewa har yanzu yana son kasar ta Yemen duk da sace su da akayi,yace sace su da akayi ba shi da alaka da taadanci,matsala ce ta cikin gida.

Tun da farko kafin tasowarsu daga Yemen, shugaban kasar ya karbi bakunci su a fadarsa inda yayi musu murnar sabuwar shekara ya kuma yi alkawarin cewa zaa hukunta wadanda

suka sace su.