1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an yan sanda a Nigeria sun kame wani ɗan jarida

Rahotani daga Nigeria sun ce, yan sandar SSS, sun capke wani ɗan jarida, na African Independent Television a ranar jiya laraba.

Ya zuwa yanzu, hukumomin yan sanda, ba su bada wata hujja ba, ta capke wannan dan jarida, mai suna Gbenga Arulegba.

An kama shi, jim kadan bayan da ya kammala shirin Focus Nigeria,daya daga shirye shiryen siyasa masu farin jini a wannan gidan telbajan.

Shugaban hukumar gudanarwa ta wannan kafar sadarwa mai zaman kanta, Raymond Dokpesi, ya bayana damuwa da wannan kamu, wanda ya danganta da ci baya, a tafiyar demokradiyar Nigeria.