1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an tsaron Sri Lanka sun kai samame a birnin Colombo

´Yan sandan Sri Lanka da sojojin kasar dauke da bindigo masu sarrafa kansu sun kai wani gagarumin samame a tsakiyar dare inda suka kame akalla mutane 900 a Colombo babban birnin kasar. Rahotanni sun ce har yanzu ana tsare da mutane sama da 50 a gidan wakafi. ´Yan sanda sun ce an kai samamen ne wanda aka yiwa lakabi da Operation Strangers Night da nufin zakulo ´yan tawayen Tamil Tigers da kuma wasu ´yan takife da ake nema ruwa a jallo. Ko da yake a shekara ta 2002 gwamnati da ´yan tawayen sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta amma wasu hare hare da ake zargin ´yan tawayen da kaiwa na barazanar sake farfado da yakin basasa a kasar.