1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamian tsaron Guinea na gasawa jamaa aya a hannu

Zainab A MohammedAugust 22, 2006
https://p.dw.com/p/Btyc
Babban birnin Guinea
Babban birnin GuineaHoto: AP

Kungiyar kare hakkin jama ta kasa da kasa watau Human Rights watch,ta gabatar da wani rahotan dake bayyana irin azabtar da jamaa da kisan gilla da jamian yansanda da sauran jamian tsaro na gwamnatin Guinea ke aiwatarwaakan jamaar da aka basu amanar tsaronsu.

Rahotan mai shafuna 30 na bayanin irin yanayi na tsare mutane a gidajen kurkukuda irin azaba da ake gallaza musu ,da kuma wasu hanyoyi da jamian yansandan na Guinea kebi na azabtar da yara matasa dake tsare a wurinsu.Wadanda ake azabtarwan dai na masu kasancewa mutane ne da suka yi wani laifi da bai taka kara ya karya ba ko kuma wadanda ke adawa da gwamnatin kasar.Da zarar an kawar dasu zuwa gidan kurkuku kuwa,akan manta dasu inda a wasu lokuta suka karasa rayuwarsu acan,cikin kangin wahalhalu na yunwa da cututtuka.

Wannan azaba da jamian tsaron na Guinea ke cigaba da gallazawa alummar daya dace su kare,na aukuwa ne adai dai lokacinda kasar ke fama da matsalolin tattalin arziki da rashin tabbas dangane da makomar siyasarta.Tattalin arzikin kasar dai na dada durkushewa,kana akwai rade radin cewa shugaban kasar Lansana Conte,ya fama da jinya matsananciya,ayayinda akwai rarrabuwar kawuna tsakanin manyan jamian sojin kasar.

Directan kula da shiyyar Afrika na kungiyar kare hakkin jamaa ta human right watch Peter Takirambudde,ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Guinea na sane da yadda jamian tsaron nata ke gasawa talakawa aya a hannu.

Kungiyar ta human Right watch dai ta gudanar da bincike inda tayiwa mutane daban daban 35,da suka hadarda kananan yara ,wadanda kuma suka yi bayanai adangane da irin azabtar dasu da jamian yansanda sukayi lokacin da suke tsare a kurkuku.Sunyi bayanin cewa ayayinda jamian yansandan ke tsare dasu,an kona su da karan taban sigari ,da wasu sinadarai masu lahani ga fa,da yankan jikinsi da ababai masu kaifi kamar reza,baya ga dukan fitar arziki,har sai sun amince dacewa sun aikata laifin da ake zarginsu da aiwatarwa.

Wani yaro mai shekaru 16 da haihuwa,myace alokacinda yansandan jke tsare dashi an daure hannunsa ta baya kana aka rataye shi akan itace yana lilo,kana jamian yansanda guda biyu suka suka cusa mata tabar sigari da wuta a hammatansa,yace bashi da niyyan amincewa da zargin laifinda ake masa,amma saboda tsabar azaba da wahala.haka ya amince da alaifinda bai san hawa ba balle sauka.

Kazalika wasu mutane 20 da suka zauna a gidajen yari fiye da shekaru 4, suna jira a gurfanar dasu gaban kotu,sun fadawa kungiyar ta human right cewa,sun amince da laifin da basu aikata bane sakamakon irin azabtar dasu da jamian yan sanda sukayi.

Adangane da hakane kungiyar ta bukaci gwamnatin Guinean data yi laakari da yancin jamaar kasar,tare da gurfanar dasu gaban kotunan sharia akan lokaci,ba tare da an tsare su fiye da kima ba.

Kungiyar tace ana samun ire iren wannan azabtarwar a yayin gudanar da gangami,musamman irin hali matsananci na rayuwa da jamaa ke ciki,inda ta bada misali da zanga zangar da ya gudana a watan yunin wannan shekara saboda tsadar rayuwa,da irin yadda gwamnati ta mayar da martani na cafke mutane.

Ya zamanto dole gwamnatin Guinea ta darajawa dokar kasa da kasa dake kare hakkin jamaa,da kuma dokar mdd ta yaki da azabtarwa,wadda kuma ke kunshe cikin kundun tsarin mulkin kasar ta Guinea.Wadannan dokoki dai na bukatar gwamnati ta darajawa yancin jamaatare da bawa kowa ikon tofa albarkacin bakinsa,ba kamar yadda jamian yansan Guinean ke take hakkin alummar kasar daya kamata su kare ba.