1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami´an tsaron Amurika sun capke ɗan tsofan shugaban shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor

April 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3Q

Jami´an tsaron Migration a Amurika, sun capke Charles Mc Arthtur Emmanuel,ɗan tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor.

An kama shi a filin saukar jiragen samar Miami bayan ya zo daga ƙasar Trinidad.

Jami´an na zargin sa da shirya ƙarya a yayin da ya bukaci, a sabinta passport ɗin sa, na Amurika.

A bayyanan da ya bada, ya ɓoye gaskiyar cewa shi, ɗan tsofan shugaban ƙasar Liberia ne.

Ranar laraba idan Allah ya kai mu, zai ƙara bayyana, gaban kotun Amurika.

A lokacin da dunia, ta yi masu shinfiɗar tabarma, Charles Mc Arthur Emmanuel,shine madugun rundunar tsaro, ta fadar shugaban ƙasa ma´aifin ,sa wanda shima, a halin yanzu, ke cikin hanun kotun Majalisar Ɗinkin Dunia, ta Siera-leone, domin ansa zargi 11, da ake masa, da su ka haɗa da aikata kissan kiyasu ga jama´a.

Ɗaya daga cikin lauyoyin tsofan shugaban ƙasa Charles Taylor, yayi kira ga ƙungiyoyi, da su taimaka masa da kuɗaɗe, domin daukar issasun lauyoyin da za su yi masa kariya.

A halin da ake cewar sa, Taylor na fuskantar ƙarancin kuɗin biyan lauyoyi.