Jami′an tsaro sunyi baratanar abkawa dalibai masu tsatsauran raayi | Labarai | DW | 04.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'an tsaro sunyi baratanar abkawa dalibai masu tsatsauran raayi

Jamian tsaro a kasar Pakistan sunyi barazanar abkawa dalibai da suke fafatawa dasu a wani masallaci a birnin Islamabad na kasar muddin dai basu saranda ba .

Shugaban daliban masu tsatsauran raayi wadanda har yanzu suke cikin masallacin na Lal yace an samu cikas a tattaunawa da sukeyi da gwamnati.

Shehunan malamai da suke shiga tsakani sun tattauna da shugabanin daliban yayinda dakarun gwamnati sukayiwa masallacin zobe.

Tun farko dai gwamnatin Pakistan ta kafa dokar hana yawo a unguwanni dake kewayen masallacin,tana mai gargadin cewa wanda ya karya wannan doka zaa harbe shi nan take.

Akalla mutane 16 suka rasa rayukansu tun jiya talata cikin fada tsakanin daliban masu tsatsauran raayi da jamian tsaro na kasar.