Jami′an tsaro sun kai samame a Bujumbura | Labarai | DW | 13.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'an tsaro sun kai samame a Bujumbura

Mutane a kalla 100 ne jami'an tsaron kasar Burundi suka kama a wani kamen kan mai uwa da wabi da suka kaddamar a unguwar Musaga da ke kudancin Bujumbura.

Da ya ke magana kan wannan batu, magajin garin birnin na Bujumbura Freddy Mbonimpa, ya danganta kame-kamen da wani mataki na neman murkushe tada kayar bayan da ake yi a wasu unguwannin birnin kusan a ko wane lokaci.

Wata mata wadda mijinta da 'ya'yanta biyu ke cikin wadanda aka kaman ta sanar cewa jami'an tsaron sun shiga har cikin gidaje inda suka yi ta kama mutane har ma da 'yan makaranta masu sanye da tufafi na 'yan makaranta. A ranar Larabar da ta gabata ma 'yan sanda da sojoji sun kama mutane fiye da 100 a birnin na Bujumbura.