1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

JAMIAN TSARO NA SHIRIN AFKAWA MASALLACIN SHIAWA A GARIN NAJAF.

To har kawo yanzu dai jamian tsaron kasar iraqi dake garin najaf na jiran umarni daga gwamnatin kasar a bagadaza,don afkawa wannan babban masallaci da shiawa ke fake.

Gwamnatin kasar iraqi ta bukaci Shugaban shiawan Muqtadr Sadr tare da magoya bayan sa dasu ajiye makamansu su firfito daga maboyar tasu,wanda idan har su kayi hakan gwamnatin ta dauki alkawarin yi musu afuwa.-

Amma muddin suka bari har gwamnatin ta bada umarnin a afka musu a fito da su daga masallacin to lallai zasu fuskanci hukunci mai tsanani.

Kamar dai yadda ministan tsaron kasar Hazem Alshaalan,ya tabbatar idan har Muqtadr Sadr bai mika wuya ba a wannan dan lokaci,to babu shakka zai fuskanci hukuncin kisa ko kuma wani hukuncin mai tsanani.

Garin na najaf a yanzu haka na cike da jamian tsaro da kuma sojin amurka wadanda suka barbazu cikin garin tare da zagaye maboyar shiawan.

Har yanzu kuwa babu alamun shiawan na shirin fitowa daga maboyar tasu,sai dai rahoton da suka fitar na cewa sun amince zasu tattauna da gwamnatin kasar don samu a warware wannan rikici.

Wanda kuma gwamnatin tace ba haka ta bukata ba,illa su fito daga maboyar su su kuma fice daga wannan gari na najaf,da aka gama illata shi sakamakon wannan rikici.

Kamar dai yadda gwamnan najaf din Adnan Alzorfi ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na AFP,cewa Muqtadr Sadr ya mai da wannan alamri kamar wani wasan yara,kuma a wannan karon babu wani tattaunawa da gwamnatin zata yi da su illa kawai a jira zuwa lokacin da aka dibar musu su fito.

Gwamnatin kasar ta bada izinin cewa idan har shiawan basu mika wuya ba daga yanzu zuwa ketowar alfijir din gobe laraba,to kawai wadannan jamiai dake zagaye da masallacin su afka ciki,tare da basu izinin suyi ta kann mai uwa da wabi.

Dubban gidaje a garin najaf yanzu haka babu kowa a cikinsu,domin kuwa tuni sojin amurka suka gargadi mazauna wannan gari musamman wadanda ke kusa da wannan masallaci dasu yi hijra zuwa wasu garuruwan don gudun bacin rana.

Wannan rikici dai ya haifar da rudani ga yan kasar iraqi,domin da yawa daga cikin su sun rasa wanda zasu zarga da haifar da wannan rikici.

Duk kuwa da gudun illata masallacin da ake yi,don gudun haifar da tashin hankali daga yan darikar shiawa dake sauran sassa na duniya a wannan karon gwamnatin kasar iraqi tace babu gudu ba ja da baya.

A garin basra wasu mutane da dama sun samu muggan raunuka,wasu uku kuma suka rasa rayukansu ciki harda wani dan karamin yaro.sakamakon wani fada da aka gwabza tsakanin shiawa da sojin britaniya a wannan gari.

A hannu guda kuma a birnin bagadaza,a yayin da wasu ministocin kasar biyu suka tsallake rijiya da baya,wasu masu tsaron su biyar suka rasa rayukansu,wasu biyar din kuma suka jikkata.

A bangaren sojin amurka kuwa,a yanzu ta kama sojin dari bakwai da goma sha shida ne suka rasa rayukansu tun bayan da rikici ya barke a kasar iraqi,kamar yadda kamfanin dillancin labaru na AFP ya bayyana.

 • Kwanan wata 24.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvh4
 • Kwanan wata 24.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvh4