1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro na ci gaba da yin sintiri a Gabon

Abdul-Raheem Hassan/AHSeptember 2, 2016

An samu asarar rayuka a sanadin bayyana sakamakon zabe a Gabon wanda Ali Omar Bango ya lashe,abin da ya janyo rashin amincewar 'yan adawar.

https://p.dw.com/p/1Jv0q
Gabun Libreville Ausschreitungen nach Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Da alama dai yunkurin manyan kasashen duniya na kwantar da hargitsin siyasar da ya kunno kai a Gabon, tun bayan ayyana sakamakon karshe na zaben da aka yi a kasrhen mako na jan kafa. Mutane kusan guda biyar ne suka mutu a tashin hankalin kuma shugaban kasar Ali Bongo da aka bayyana samun nasaransa a zaben, ya bayyana takaicin yadda rayukan 'yan kasar ke salwanta da ma yadda aka kona majalisar dokokin kasar.

"Wannan gidan majalisa, na daya daga cikin gine-gine da 'yan kasar Gabon za su yi alfahari da shi, a don haka banga abin da ya hada kalubalantar sakamako da kona gidajen al'umma har ma gidan majalisa ba."

Shugaba Ali Omar Bango ya ce za a hakunta masu laifi

Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewar har ya zuwa wannan lokaci, 'yan sanda na ci gaba da tsare da wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa da wasu shugabannin kungiyoyin al'umma. A gefe guda kuma ministan cikin gida na kasar Gabon, ya ce an fadada kamen da a yanzu ya kai ga tsare masu tada zaune tsaye da sunan zanga-zanga har mutane sama da 1,000. To sai dai Shugaba Ali Bongo, ya jadda cewar doka za ta yi aiki.

Gabun - Präsident Ali Bongo Ondimba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Yalcin

"Babu wanda ya fi karfin doka duk wanda ya yi laifi a fili take za a hukuntashi."

Gabunischer Politiker Jean Ping
Hoto: Getty Images/AFP/K. Tribouillard

Martanin jagoran 'yan adawar Jean Ping a game da abin da ke faruwa

A yanzu dai mukarraban gwamnatin shugaba Ali Bongo, sun bukaci madugun adawar da ya tsawata wa magoya bayansa da ke ci gaba da zanga-zanga. To sai dai, a wata hira ta musamman da tashar DW ta yi da Jean ping, ya bayyana daukar shawar sauran kasashen duniya na sake kidaya kuri'u.

"Abin da muke bukata shi ne wanda dukkanin sauran shugabannin kasashen duniya suka ba da shawara shi ne na sake lisafa kuri'u "