Jami´an tsaro Jamus sun cafke wani dan Iraqi bisa zargin aikin ta´addanci | Labarai | DW | 11.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an tsaro Jamus sun cafke wani dan Iraqi bisa zargin aikin ta´addanci

´Yan sanda a nan Jamus sun kame wani dan Iraqi da ake zargi da yada fafayan bidiyo da na kaset masu dauke da jawaban shugabannin kungiyar al´Qaida ta intanat. Mutumin wanda ya shiga hannun jami´an tsaro a birnin Osnabrück, ana zargin sa da buga jawabai na Osama Bin Laden da Ayman al-Zawahiri da kuma Abu Musab al-Zarqwawi a cikin shekara guda da ta gabata. Masu shigar da kara a birnin Karlsruhe mazaunin kotun kare kundin tsarin mulkin Jamus sun ce ta haka mutumin ya marawa ayyukan ta´addanci baya. Mutumin wanda aka ba da sunansa da Ibrahim R, a yau zai gurfana gaban kotu.