Jamian tsaro da na NATO a Afghanistan sun kwace garin Bakwa daga hannun yan Taliban | Labarai | DW | 20.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamian tsaro da na NATO a Afghanistan sun kwace garin Bakwa daga hannun yan Taliban

Rundunonin tsaro a kasar Afghanistan tare da taimakon dakarun kungiyar NATO sun sanarda kwace garin Bakwa dake hannun yan taliban a yammacin kasar.

Gwamnan lardin Farah Mujahiddin Baluch yace sojoji da yan sandan Afghanistna kusan 200 suka kai farmaki garin na Bakwa bayanda yan kungiyar Taliban suka kame garin a ranar litinin,wannan dai shine karo na biyu da cikin wannan wata da yan taliban suka kame wasu larduna biyu daga hannun gwamnati.

A halinda ake ciki kuma rundunar sojin Amurka ta sanarda mutuwar wani sojanta a lardin Kunar a jiya litinin.

Ya zuwa yanzu dai akalla sojojin Amurka 297 suka rasa rayukansu a kasar ta Afghanistan tun lokacinda Amurkan ta mamaye kasar a 2001.

A wani labarin kuma rundunar sojin ta Amurka tace ta jefa bam mai nauyin kilogram 910 kann wani kogo da ake zaton yan kungiyar Taliban suke boye ciki a lardin Uruzgan.