1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAMIAN TSARO A GARIN NAJAF.

Maryam L.Dalhatu.August 24, 2004
https://p.dw.com/p/Bvh5
Rikici ya illata garin najaf.
Rikici ya illata garin najaf.Hoto: AP

Kusan makwanni uku kenan ana ta dauki ba dadi tsakanin shiawa da kuma sojin amurka a garin najaf na kaasar iraqi,bayan gaza cimma daidaito da akayi a karo na biyu,tsakanin gwamnatin kasar da kuma shiawan.

Sai a yau ne kuma rana ta ashirin da wannan rikici gwamnan wannan gari na najaf Adnan Alzorfi ya nuna bacin ransa game da yadda rikicin ya illata wannan gari tare da watsa mazauna garin zuwa wasu sassan kasar.

A cikin jawabin nasa ne ya bayyana cewa jamian tsaron kasar iraqi,a shirye suke su afkawa shiawan dake boye a cikin masallacin idan har basu ajiye makamansu sun mika wuya ba.

A yau dai an wayi gari tankunan yakin amurka na ta kutsowa cikin garin najaf,bayan fidda su da aka yi a cikin makon daya gabata.haka kuma a karo na farko gwamnatin kasar iraqi ta dauki matakin sanya jamian tsaron ta wajen kokarin kawo karshen wannan rikici.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa a yanzu haka wadannan jamian tsaro na cikin garin na najaf kuma suna zagaye da wannan masallaci,suna jiran izinin afkawa daga gwamnatin kasar a birnin bagadaza.

Kamar yadda a baya aka jaddada cewa babu wani sojin amurka da zai shiga harabar wannan masallaci,a wannan karon ma haka abin yake,sai dai fa za ayi amfani da su wajen zagaye masallacin don gudun bacin rana.

Adnan Alzorfi gwamnan garin najaf,tare da ministan tsaron kasar iraqi,Hazem Alshaalan,sun ki bayyana lokacin da ake shirin afkawa wannan masallaci sai dai sun ce hakan zai faru nan da yan saoi kadan.

A wata sabuwa kuma ministocin kasar iraqin biyu ne suka tsallake rijiya da baya,sakamakon harin da aka kai musu a safiyar yau talata.

Ministan muhallin iraqi,Mishkat Almoumin,shi ya fara tsallake wannan rijiya da baya,da misalin karfe takwas na safiyar yau.hakan ta faru ne sakamakon afkawa wata mota dauke da boma bomai da wata motar tayi a yayin da motocin ministan ke kokarin wucewa.mutane hudu ne suka rasa rayukan su wani daya kuma ya samu rauni,sakamakon hakan.

Mintuna talatin bayan wannan ne kuma wani bomb din ya tashi a kusa da ofishin ministan ilmin kasar Sami Almudhaffar,a yayin da motocinsa ke kokarin tsayawa a kofar ofishin,mutum daya ne ya rasa ransa wasu biyu kuma suka jikkata a wannan karon.

Ana dai zargin wata kungiyar yan tawaye ce dake karkashin jagorancin Abu Musab Alzarqawi,na kungiyar alqaeda.da kai wadannan hare hare,duk kuwa da cewa babu tabbacin hakan.

Duk da wadannan tashe tashen hankula dake faruwa a kasar ta iraqi,sai gashi taki amincewa da kiran da kasar iran tayi mata da sauran makwabtan ta don samar da hanyoyin da zasu taimaka wajen kawo karshen wannan rikici na najaf.

Kamar yadda ministan harkokin wajen iraqi Hoshiyar Zebari,ya bayyana,wannan rikici na najaf ba abu ne da ya shafi wasu kasashen ba,yace rikici ne na cikin gida tsakanin gwamnatin kasar da yan kasar.

Bisa hakan ne kuma ya jaddada cewa kawo karshen wannan rikici abu ne da zaa yi shi bisa dokoki da kaidojin kasar iraqi,amma ba na wata ko wasu kasashen ba.

A yanzu haka dai a garin najaf,jamian tsaron kasar na jiran izini daga bagadaza na afkawa cikin wannan masallaci don fiddo shiawan ta karfin tsiya,sai dai ana jira a gani ko kafin wannan lokaci shiawan zasu mika wuya su fito daga maboyar tasu.