Jami′an Siyasar Afirka na ajiyar satattun kuɗaɗe a Amurka | Siyasa | DW | 08.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jami'an Siyasar Afirka na ajiyar satattun kuɗaɗe a Amurka

Matsalolin cin hanci da rashawa tsakanin Jami'an gwamnatin Afirka na cigaba da durkusar da nahiyar

default

Atiku Abubakar

Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa tayi kira ga gwamnatin Barack Obama na Amurka, data aiwatar da shawarwarin dake kunshe a wani rahoton bincike, domin taimaka wajen dakatar da ajiyan satattun kuɗaɗe dake kwarara zuwa Amurkan daga 'yan siyasar ƙasashen waje, musamman Afirka.

Mai fafutukar kare hakkin Jama'a a tarayyar Nigeria Shehu Sani yayi tsokaci game da irin kuɗaɗen da jami'an siyasa a Afirka ke sacewa suna kaiwa domin ɓoyewa a ketare, sakamakon binciken da Amurka ta gabatar.

'Yan majalisar Dottijan Amurka Carl Levin da Tom Coburn waɗanda suka gudanar da binciken sun gabatar da rahoto mai shafuna 330 mai "taken kawar da rashawar ƙasashen ketare daga Amurka" wanda bayanin yadda jami'an gwamatocin Angola,Equitorial Guinea, Gabon da Nigeria, suka cimma nasarar shigar da miliyoyin daloli zuwa cikin Amurkan domin ajiya, tare da tallafin lauyoyi, wasu mutane, da hukumomin dake kula da harkokin kuɗi.

Nigeria Unruhen Flüchtlinge bei Jos

Talauci tsakanin al'umma

Tsohon mataimakin shugaban tarayyar Nigeria Atiku Abubakar na ɗaya daga cikin jerin mutanen da aka gudanar da bincike akansu. Inda akace tsakanin shekarata 2000 zuwa 2008 kadai, shi da mai ɗakinsa sun shigar da dala miliyan 40 zuwa cikin Amurka domin ajiya. Tare da bada cin hancin dala miliyan 14 wa Jami'ar Amurka dake Washinton DC, domin musayar bayanai dangane da Jami'ar dashi Atikun ya kafa yan a jihar Adamawan Nigeria.Ko mene illolin waɗannan kuɗaɗe da ake sacewa daga cikin ƙasa musamman kan rayuwar al'ummomin ƙasa.

Satan kuɗi domin kaiwa ajiya a ketare ba wani sabon labari bane a ɓangaren 'yan siyasan Afirka musamman Nigeria. Domin a yanzu bawai Amurka ko Turai Jami'an gwamnatin Nigeriyar ke kai satacciyar ajiyar ba, amma ƙasashen Larabawa da Asia inji Shehu Sani.

A cewar mai fafukar kare hakkin bil'adama Shehu Sani dai mafita ɗaya iatace, kafa kotun ƙasa da ƙasa wadda zata hukunta irin wadannan ɓarayin dukiyar ƙasa, kamar yadda ake da ta shari'ar masu miyagun laifuffukan yaƙi a birnin Hague. Kana akwai bukatar samun haɗin kai daga ɓangaren hukumomin ketare kamar Turai dana Ƙasahen Larabawa, inda nan jami'an gwamnatin ke ɓoye satattun kuɗaɗen.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Yahouza Sadissou